Masana na mahawarar dacewa ko rashin dacewar martanin da shugaba Jonathan ya mayarwa tsohon shugaba Obasanjo kan wasikar da ya rubuta masa.
WASHINGTON, DC —
Kwanan nan shugaba Jonathan ya mayarwa tsohon shugaba Obasanjo martani dangane da wasikar da ya rubuta masa wadda ta tayar da kura a cikin kasar Najeriya.
Masana harkokin siyasa na ganin dacewa ko rashin dacewar martanin da shugaba Jonathan ya mayarwa shugaba Obasanjo bisa ga wasikar da ya rubuta masa. Masanin kimiyar siyasa Dr. Sadiq Abba ya nazarci martanin. Ya ce Jonathan na cikin wani hasari. Koyaya Obasanjo yake yana da anfani. Fadan da Jonathan yake yi da su Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar da gwamnoni da 'yan majalisu ba alheri ba ne gareshi. Fadan zai kawo mashi cikas idan yana neman zabe.Kuma Obasanjo ba mutumin da yake yafewa ba ne. Idan aka takashi sai ya muguwar ramuwa. Abun da Obasanjo yake shiryawa da abun da wasu suke yi zasu sa su yiwa Jonathan wuya ya sake cin zabe a shekarar 2015. Yana iya ya samu tikitin PDP amma idan ire-iren su Obasanjo suka marawa wani baya ba zai kai labari ba.
Dattawan PDP na juyayin yadda gimshikan jam'iyyar ke tone-tone da rubutawa juna wasika. Dan kwamitin zartaswar jam'iyyar Isa Tafida yana ganin dai sulhu shi yafi a'ala.Da wasikar da aka rubutawa Jonathan ya yi hakuri. Da wasikar da aka rubutawa Obasanjo shi ma ya yi hakuri. Su mayarda zuciya nesa. Najeriya na bukatar cigaba. Babu wanda yake son kasar ta cigaba irin Jonathan. Shugaba ne mai hakuri da hangen nesa. Amma babu wanda ya wuce kuskure.Shi ma Obasanjo shugaba ne kuma uba ne. Don haka idan yana da abun da yake so ya kirasu ya fada masu.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5