WASHINGTON, DC —
Ra’ayoyi na ci gaba da shan banban akan amsar da shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya maida wa tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo. A wasikar farko, shugaba Obasanjo ya zargi shugaba Jonathan da laifukka da yawa da suka hada da cewa yana neman maida hannun agogo baya a fannoni daban na rayuwar ‘yan Nigeria, ciki har da maganar demokradiya, tattalin arziki da sha’nin tsaro. Sai dai kuma an sami sabanin ra’ayi a amsar da shi Mr. Jonathan ya maida ga wannan wasikar. Ga wasu daga cikin ra’ayoyin da wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz ya dauko mana kan lamarin:
‘Yan Nigeria sun maida murtani ga amsar da shugaba Jonathan ya maida akan wasikar Obasanjo.