Waɗanne irin ɗabi'u da halaye ya kamata matasa samari da 'yan mata su dauka kuma su kiyaye domin samun kyakkyawar dorewar soyaya?.
A cewar wata matashiya Isha'u Aminu Haris daga gandun albasa dake jahar Kano ta bayyana ra'ayin ta inda ta ce lallai idan 'ya mace zata fitar da kwadayi to bazata fuskanci wulakanci ba. ta kara da cewa gaskiyar mutum bata karewa, dan haka zama da juna cikin gaskiya da rukon amanar juna ne maganin wannan lamari.
Yawancin dalilan da suke sa masoya su fara canza hali sun hada da rashin gaskiya, da cin amana, matashiyar ta kara da cewa yawancin lokaci samari kan shirga ma 'yan mata karyar cewa ba su da wasu 'yan mata bayan kuwa ba gaskiya bane. Ta ce wani loacin kuna tare wayar sa zata fara ringin amma bazai iya dauka ba saboda tsabar rashin gaskiya.
Da muka waiwaya ɓangaren matasa kuma, mun tattauna da wani matashi mai suna Abbas Adamu Abubakar wanda ya bayyana na sa ra'ayin da cewa yakamata matasa su rika tunanin cewar kyalkyali fa ba abin da za'a dogara a kansa bane dan gujewa da na sani.
Matasa masu sa kan su cikin irin wannan jarabar kwadiyi na cikin matasala domin kuwa masu iya magana sun ce idan akwai kwadayi to lallai akwai wahala.
Ku biyo mu a shafin mu na facebook/dandalinvoa domin tafka muhawara.
Saurari cikakken bayani.