Kwamitin zartaswa na hukumar kwallon kafar najeriya NFF, yace a koda yaushe membobin hukumar na baiwa shugaba Amaju Pinnick goyon baya da kwarin gwiwa.
Jami’in yada labaran hukumar kwallon kafa ta Najeriya Suleiman Yahaya-Kwande, a jiya Alhamis ne yake bayanin yadda kwamitin hukumar ke yabawa da ayyukan Pinnick. Inda yace “idan da zaka duba cigaban da aka samu tun da Amaju Pinnick ya karbi shugabancin hukumar wato shekara guda da ta wuce, tabbas za’a yaba masa. Abin mai kyau anan shine yana hada kowa da kowa a cikin duk abinda yake yi, yana kuma sauraron duk abinda kowa yake dashi na fada.”
Ya ci gaba da cewa a koda yaushe ina matukar jin dadin zuwa taro da shi, saboda shugaban na baiwa kowa mutunci sa, yana kuma kawo muhimmam shawarwari domin a yi muhawara kansu.
Yakuma tabbatar da cewa zasu fitar da wasu shirye shirye da suke dasu ga hukumar kwallon kafar Najeriya, da suke tsammanin mutane zasu ji dadin su. Sati mai zuwa dai zasu fitar da sanarwar wani shiri na ci gaban matasa.