Da Wuya Iran Ta Ci Gaba Da Mutunta Yarjejeniyar 2015- Rouhani

Shugaban Iran Ayatollah Ali Khomenei

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce idan kasashen da suke cikin yarjejeniyar 2015 basu saka wani jari a kasar ba, da wuya ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar saboda takunkumin da Amurka zata kakaba mata

Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani yace zaiyi wahala kasar taci gabada tsayawa cikin yarjejeniyar makaman nukiliya ta shekarar 2015 da aka sa hannu da kasashen duniya, muddin ba zata anfana ba daga wannan yarjejeniyar.

Rouhani ya fadawa shugaban Faransa Emanuel Macron ta wayan tarho cewa sauran kasashen dake da sa hannun su a wannan yarjejeniyar irin su Birtaniya,Jamus, Rasha,da China wajibi ne su samu hanyar da zasu saka wa kasar ta Iran babban jari bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke shawarar ficewa daga yarjejeniyar tare da kakaba wa Iran din wasu takunkumi.

Trump ya ce Amurka ta fita ne domin yarjejeniyar ta raja’a a gefe guda, Iran ce kadai zata anfana fiye da sauran kasashen.

Shawarar da ya yanke na fidda Amurka daga wannan yarjejeniyar a cikin watan Mayu, ta bar Faransa,Jamus, Birtaniya, suna ta kokarin ganin cewa Iran ta samu wadatattun kudi da kulawa domin kawai ta ci gaba da tsayawa cikin wannan yarjejeniyar.

Jami’an Faransa sun nuna alamar, sauran kasashen dake da hannu a wannan yarjejeniyar zasu yi wata ganawa nan ba da jimawa a birnin Vienna.