Da Karamin Jari, Yau Inada Rufin Asiri Babu Bani-Bani

Amina Omar

Amina Umar – da karamar sana’ar sayar da Gadaje, Katifu da Kujeru, wanda ya kaita ga mallakar Gidaje har guda biyu bayan ta kama sana’ar dogaro da kai.

Malama Amina ta ce ta fara sana’ar hannu ne tsawon lokaci, tun tana sayar da kananan abubuwa na kulle kulle na mata a gida kamar su kayan miya, sikari da sauransu.

Ta ce a yanzu lokaci yayi da mata zasu tsaya kan kafafunsu, domin zamo masu dogaro da kai don hucewa kai takaicin zaman duniya, ta kara da cewa da kananan kudade sai da ta tara jari na naira dubu ashiri.

Daga dubu ashiri sai da jarinta suka kai naira dubu arba'in, har ta kai ga ta ga sayan fili, daga nan tana dai cikin sana’ar har ta samu mallakar gidaje guda biyu sakamakon sana’ar hannun da ta rike.

Daga cikin kalubalen da ke ci mata tuwwo a kwarya ta ce mafi yawa shine, yawan karuwar bashin ko rashin cika alkawari daga wajen masu sayen kaya da take fuskanta.

Malama Amina ta ce duk macen da bata rike sana’ar hannu ba, tana tare da kuncin rayuwa, inda take jan hankali mata da su mai da hankali wajen kama sana’ar hannu.

Your browser doesn’t support HTML5

Da Karamin Jari, Yau Inda Rufin Asiri Babu Bani-Bani 5'10"