Da Dangari: Tarihin Zangon Tungar Malam, Ghana

Bandiagara, Mali.

Shirin Da Dangari na wannan makon ya kai ziyara zangon Tungar Malam da ke kan hanyar zuwa Cape Coast a yankin Greater Accra da ke kasar Ghana, wanda Idris Abdallah Bako na Alpha Rediyo Kumasi ya gabatar.

Washington, DC - Galadiman zangon Tungar Malam Alhaji Ali Garba ya ce tarihi ya nuna a shekarar 1845 aka kafa garin Tungar Malam.

Wani mai suna Jibrin, dan asalin jihar Kano a Najeriya ne ya kafa garin wanda da farko ake kira Tungar Malam Jibrin.

Garin Tungar Malam dai ya yi suna wajen sana’ar kamun kifi, noma, kiwo da harkar rini kafin zuwan ilimin boko.

Alhaji Garba ya kuma ce babban kalubalen da suke fuskanta a zangon shi ne matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da wasu matasa ke yi.