Garin ‘Yandaki dai fulani ne suka kafa shi a shekarun aluf dari hudu da hamsin da wani abu, gari ne mai ganuwa da aka gina saboda kariya daga kamen bayi a lokacin, a cewar Dr. Kabir Umar Musa ‘Yandaki na jami'ar 'Yaraduwa da ke Katsina.
Garin na da alaka da masarautar Katsina. Akwai lokacin da wani sarkin Katsina ya gina wani “Dandaki” a garin don zuwa ya huta, asali kenan aka samu sunan garin “‘Yandaki,” a cewar Dr. Kabir
Garin ya shahara wajen noma, kiwo da kuma kasuwanci, bayan haka yana kuma tunkaho da masu ilimi na addini da kuma na boko.
Sai dai Dr. Kabir ya ce babban kalubalen da garin ke fuskanta shine matsalar ruwan sha.
Saurari cikakken shirin wanda Abdurrahaman Kabir Jani ya gabatar.
Your browser doesn’t support HTML5