Shirin Da Dangari na wannan makon ya kai ziyara garin Tsanni da ke karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina a Najeriya.
WASHINGTON, D.C —
A wata hira da Abdul Kabir Jani, magajin garin Tsanni Bello Mu’azu ya ce wani da ake kira Malam Ibrahim Iggi, da ya zo daga Timbuktu ne ya fara sarautar garin Tsanni a shekarar 1804. Wannan gari dai ya shahara wajen sana’ar noma da kiwo sai kuma ilimi.
Daya daga cikin kirarin da ake yi wa ‘yan garin shi ne “Tsanni kowa sarki,” domin kuwa ‘yan garin ba sa jin tsoro kuma sun yi suna wajen takadarci a baya.
Saurari cikakken shirin da Abdul Jani ya gabatar.
Your browser doesn’t support HTML5