Gidan Rediyon Nagarta a jihar Kaduna ya lalubo tarihin garin Farakwai da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
WASHINGTON, DC - Garin Farakwai dai gari ne mai tsohon tarihi da aka kafa kafin Zangon Aya da garin Yalwa, a cewar Basaraken garin Muhammad Labaran.
Basaraken ya ce kabilar Gbagyi ce ta fara kafa garin Farakwai, bayan da suka yi kaura sai kabilar Jaba ta yi sarautar garin zuwa wani lokaci.
A shekarar 1888 Fulani suka karbi sarautar garin Farakwai, wato a shekarun da Umaru Dan-Aliyu ya karbi sarautar, a cewar Labaran.
Noma, kiwo, da saka su ne sana’o'in da aka san garin Farakwai da shi.
Saurari cikakken shirin da Nasiru Yakubu Birnin Yero ya gabatar.
Your browser doesn’t support HTML5