A cigaba da akeyi a wasannin firimiya lig na shekaraR 2016/17 a tarayyar Najeriya, inda aka share makonni 37 ana gwabzawa, a ranar lahadi 3/9/2017 aka buga wasannin mako 37 kamar haka.
Sunshine 4-0 Ifeanyi Ubah, Lobi Star, 1-0 Niger Tornadoes, Shooting Star, 1-0 Akwa United, Kano Pillers, 2-0 El-kanemi, MFM Fc, 2-0 Nasarawa United, ABS, 2-1 Abia Warriors.
Sauran wasannin sun hada ta Rivers United, 3-0 Gombe United, sai Enugu Ranger, 1-1 Enyimba, Kastina United, 3-0 Remo, Wikki Tourist, 1-0 Plateau United.
Duk da rashin nasara da Plateau United, ta yi tsakaninta da Wikki Tourist a garin Bauchi, har yanzu Plateau, ce kan gaba a saman teburin na NPFL na bana, inda take gab da lashe gasar.
Plateau united, dai tana da maki 63 a mataki na daya sai mai biye mata MFM, ta garin Lagos, da maki 62, Enyimba, tana mataki na uku da maki 58 Akwa United, a mataki na hudu da maki 57, sai Kano Pillars, da maki 54.
Kungiyoyi biyar kuwa suna tafiya a jere ne duk makinsu dai-dai kamar haka:
Lobi Star, maki 53
Nasarawa, 53
Ifeanyi Ubah, 53
Enugu Rangers, 53 sai
El-kanemi 53
Akwai kungiyoyin da suke tsaka mai wuya kamar haka
Rivers United, maki 52,
Kastina United, 52
Sunshine 51,
Niger Tornadoes, 51
Abia Warriors 50
Shooting Star, 50
Wikki Tourist 50,
Abubakar Bukola Saraki, maki 49,
A cikin wayannan kungiyoyi da suke tsaka mai wuya za'a janyo biyu domin Komawa gasar kasa da Firimiya.
Kungiyoyi biyu kuwa tuni sun fice daga gasar Firimiyar ko da sun samu nasara a sauran wasa daya da ya rage musu, wadannan kungiyoyi sune Gombe United, da take mataki na goma sha tara da maki 43, sai Remo, wace take kasan teburin a mataki na ashirin da maki 29.
Ranar Asabar 9 ga watan Satumba na 2017 din nan za'a karkare gasar ta Firimiyar Najeriya ta bana.
Your browser doesn’t support HTML5