Hakan ya kara bayyana ne yayin da jam’iyyar ta nada gwamna Aminu Tambuwal a matsayin babban daraktan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
An tabbatar asalin rikicin na cikin gida na PDP ya faro ne daga marawa Atiku baya da Tambuwal ya yi ta hanyar janye takara a zaben fidda gwani a dandalin zaben, inda hakan ya bai wa Atikun tagomashi ya yi nasara kan Nyesom Wike.
Wike wanda ya yi watsi da matakin shugaban kwamitin amintattu na yin murabus don kujerar ta koma kudu ta yadda hakan zai rage zaman doya da manja, ya ce saukar shugaban jam’iyyar ne kawai zai kwantar da kurar don ba zai yiwu dan takara da shugaban jam’iyyar duk su fito daga arewa ba.
Babban mai taimakawa shugaban jam’iyyar Yusuf Dingyadi ya ce sun riga sun ja layi daga ci gaba da wannan cece-kucen, don jam’iyyar ba ta mutum daya ba ce.
In za'a iya tunawa, tsohon shugaban kwamitin amintattu na PDP, Walid Jibrin, ya ce ya sarayar da matsayin sa, inda zai rika ba da shawara daga bayan fage.
PDP ta nada gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zabe, yayin da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da Bala Muhammad na Bauchi ke zaman mataimaka daga kudu da arewa kenan.
Shin Wike mai samun goyon bayan wasu gwamnonin da su ka hada da Samuel Otom na Binuwai, zai ja da baya ko zai ci gaba da kai ruwa rana?
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5