Da Alamar Sufeto Janar 'Yan Sandan Najeriya Zai Ci Gaba Da Aiki

Sufeto janar

A Najeriya Ana ci Gaba da cece kuce kan wa'adin sufeto Janar na yan sandan kasar Ibrahim Kpotum Idriss. Yayin da wani sahsen ‘yan Najeriya suka gani zai iya ci gaba da aikinsa musamman a wannan lokacin siyasa, wasu kuma na gani lada ya isa.

Shi dai shugaban ‘yan sandan tun ranar uku ga watan Janairun nan ne yake cika shekaru 35 a yana aikin dan sanda, al'amarin da kundin tsarin dokokin Najeriya ya bukaci dole ma’ikaci ya aje aiki bayan ya kwashe shekaru 35 a cikin aikin.

A bisa tsarin mulki, shugaban kasa na da hurumin kara wa'adin sufeto Janar din, amma har yanzu Shugaba Muhammadu Buhari bai ce komai ba kan batun, al'amarin dake ci gaba da janyo cece-kuce tsakanin Jama'ar kasar.

Majalisar shugabannin matasan Arewacin Najeriyar na ganin duba da yadda kasar zata shiga zabe, akwai bukatar a karawa shugaban yan sandan lokaci.

Shugaban majalisar matasar Arewar Comrade Elliyat Afiyo ya ce duba da halin da kasar ke ciki da kuma irin rawar da Ibrahim Idriss ya taka, to akwai Bukatar a mai karin wa'adi.

Amma masanin tsaro, Mallam Kabiru Adamu na ganin lalle an sami tabarbarewar tsaro a zamanin mulkin wannan shugaban ‘yan sanda musamman wajen hauhawar fashi da makami da satar mutane da fadan makiyaya da manoma.

Wakilinmu Hassan Maina kaina ya shirya mana rahoto a kan wannan batu daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

SUFETO JANAR ZAI CI GABA DA AIKI