Da alama za a jinkirta bikin ba da lambar yabo mafi muhimmanci ta shekara mai zuwa saboda rashin fitar da wasu shirye-shirye a kan lokaci sanadiyar annobar coronavirus.
Wani labari da aka fitar jiya Talata a wata mujallar shakatawa, an ruwaito wani da ba a bayyana sunansa ba yana cewa “watakila” a dage bikin da ake gudanar wa shekara-shekara, wanda aka shirya yadawa ranar 28 ga watan Fabrairu ta gidan talabijin na ABC-TV.
Amma wata majiya na cewa, ba'a bayyana dukkan bayanan da aka shirya ba. Karkashin dokokin kungiyar da ke daukar nauyin bayar da lambar yabon, dole ne sai an fitar da shirin Fim kamar yadda aka saba ta gidan cinema kafin ranar 31 ga watan Disamba, idan har ana son tantance shi domin lambar yabo ta Oscar.
Amma an rufe dubban gidajen cinema saboda annobar coronavirus, yawancin fina-finai basu samu an fitar da su ba kamar yadda aka saba, sai dai ta yanar gizo kamar shafin Netflix, wadda ke neman kungiyar ta sauya ka’idojinta wajen baiwa fina-finanta damar shiga wannan gasa.