Cynthia Rufe: "Mun Damu Da Yadda Ake Sukar Alkalai"

Shugabar Kungiyar Alkalan Kotunan Tarayya A Amurka - Cynthia Rufe

Shugabar Kungiyar Alkalan Kotunan Tarayya A Amurka - Cynthia Rufe

Kungiyar Alkalan kotunan Tarraya a nan Amurka, za ta yi wani taron gaggawa a gobe Laraba, bayan da ta yi zargi jami’an ma’aikatar shari’ar kasar da yin katsalandan a wata kara da ta shafi wani babban aminin Shugaba Donald Trump.

Shugabar kungiyar, Mai Shari’a Cynthia Rufe ce ta shaidawa Muryar Amurka hakan, inda ta ce sun kira taron ne saboda sun damu da yadda ake sukar alkalai.

Wannan batu, shi ake tunanin zai mamaye taron.

Ko da yake, ta kaucewa fadada bayananta, mai Shari’ar ta ce, ba za su iya jira har sai lokacin taron da suka saba yi a farkon hunturu ba, shi ya sa suka kira taron a yanzu.

A makon da ya gabata ne dai ma’aikatar shari’ar Amurkan ta shammaci jama’a ta nuna sassauci ga Roger Stone.

Roger Stone Tare Da Matarsa

Roger Stone Tare Da Matarsa

An samu Stone da laifin yi wa majalisar dokoki karya da kuma hana doka ta yi aikinta a lokacin binciken shisshigin da Rasha ta yi a zaben Amurka.

Masu shigar da kara sun nemi kotu ta yanke ma shi hukuncin shekara bakwai zuwa tara, hukuncin da ya kamaci irin wadannan laifuka.

Amma ma’aikatar shari’ar ta nuna sassauci ga Stone bayan da Shugaba Trump ya shiga shafin Twitter ya yi korafin cewa hukuncin shekara bakawai ya yi tsauri, sannan ya ce an yi rashin adalci.

Shi dai Stone babban aminin Shugaba Trump ne.