Mr Emmanuel ya bayyana cewa rashin lafiyar ta mamaye daukacin sansanin, kuma ya yi Karin bayanin cewa basa samun wani taimako baya ga dogaro da tallafin da suke samu daga masallatai da coci-coci da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu dake kewayen birnin na Abuja.
Ya kara da cewa sun yi iya bakin kokarinsu domin neman taimako daga gwamnati data gina masu dakin shan magani amma mutanen dake tausayin su ne kadai ke kai masu dauki musamman ma a wannan mummunan hali da suke ciki.
A yayin da wakilin sahsen Hausa na muryar Amurka Hassa Maina Kaina ya sami zantawa da shugaban sansanin, ya sami labarin cewa kungiyar kai daukin gaggawa mai zaman kanta ta babban birnin tarayya ta kai taimako a sansanin na Kuci Goro, kuma ya ji tabakin Alhaji Abbas Idris, jagoran humar inda ya ce,
“A gaskiya mun tura masu bincike akan kula da harkokin lafiya kuma sun bayyana mana cewa lokacin damuna ne kuma lallai akwai wannan matsala a sansanin, kuma a yanzu haka da muke Magana da kai bai wuce sa’o’I uku ko hudu ba da muka rarraba masu maganin zazzabin cizon sauro ba a dukkan sannsani, daman akwai wata kungiya data bada wannan taimako kuma mun rarraba masu harda gidan sauro.”
Hajiya Fatima Kyari Muhammed ce jagorar wata kungiya mai zaman kanta kuma mai suna likesmind project ta bayyana cewa lamarin yafi karfin ita kanta gwamnati, shiyasa dolr ne kungiyoyi kamar nasu da kuma na kasa da kasa su kai dauki.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina Daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5