Bincike ya nuna har yanzu ana fama da cutar tamowa a jihar wadda ta samo asali daga karancin ingantacen abinci mai gina jiki.
Abu Yahaya babban darakta na ma'aikatar kiwon lafiya a jihar Damagaran yace an yi bincike tare da nazari an tabbatar jihar Damagaran ce ke kan gaba a cutar tamowa. Yace a ce su ne suke kan gaba a cutar tamowa bashi da dadin ji saboda haka suka tashi su nemi hanyar shawo kan cutar. Duk inda suka yi kuskure zasu gyara kuma duk yaron dake fama da cutar ya je ya ga likita.
Babbar matsalar da likitoci suka gano itace sakacin iyaye na rashin yin anfani da maganin da ake basu. Wani lokacin idan an ba yaran magunguna sai iyayen su bi wata hanya su sayar. Yaron da yakamata ya yi wata daya ko biyu yana shan maganin domin ya warke amma sai yi shekara daya bai samu lafiya ba. Wasu iyayen basa anfani da magungunan yadda ya kamata. Abu na biyu shi ne toshe hanyar da iyaye ke bi suna sayar da magungunan.
Abu Yahaya ya cigaba da cewa zasu dauki duk matakin da ya dace domin magance matsalar da zummar kawo karshen tamowa a jihar. Zasu shiga garuruwa su samu sarakuna su yi masu kuka kan matsalar domin su taimaka al'ummarsu ta sake hali. Duk yaron da aka ba maganin tamowa mai garin da ma'aikatan kiwon lafiya zasu bi uwar su tabbata ta ba yaron maganin yadda ya kamata.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5