Cutar Sankarau Na Ci Gaba Da Hallaka Jama’a A Jihar Neja

Kawo yanzu gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutane goma sha shidda daga cikin mutane talatin da daya da suka kamu da cutar sankarau a wasu kananan hukumomi guda hudu dake cikin jihar Neja.

Kananan hukumomin sun hada da Agwara, Rijau, Magama da kuma karamar hukumar Kontagora.

A wani taron manema labarai a yammacin talatannan data gabata, kwamishinan lafiya na jihar Neja, Dr Mustapha Jibril, ya ce lamarin fa ya yi matukar tayar da hankalin jama’a, bisa la’akari da yadda lamarin cutar ke kara ta’azzara.

Ya ce “yanzu a kananan hukumomi hudu muna da mutane talatin da daya da suka kamu da wannan cuta, kuma gaskiya abin bai yi mana dadi ba domin kawo yanzu mun rasa rayukan jama’a goma sha shidda, domin yawancin jama’a sun yi tunanin mayu ne suke hallaka jama’a shiyasa basu damu da zuwa asibiti ba, wannan ita ce babbar matsalar da muke fuskanta”

Daga karshe ya bayyana cewa zasu ci gaba da wayar da kan jama’a da kuma hada kai da masu magungunan gargajiya domin fadakar da jama’a musamman masu zuwa wurinsu nemen magunguna.

A yanzu haka dai kwamishinan lafiya Dr Mustapha Jibril, ya ce sun tura jami’an lafiya dauke da magunguna da kuma fadakarwa ga jama’a akan kaucema kwana cikin zafi da kuma cinkoson jama’a domin tabbatar da an tsayar da yaduwar cutar.

Rahotanni sun nuna cewa cutar na ci gaba da yin barazana a wasu jihohi guda ashirin dake fadin Najeria, lamarin da ke nuna akwai bukatar daukar matakin gaggawa domin ceto rayukan jama’a.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Sankarau Na Ci Gaba Da Hallaka Jama’a A Jihar Neja