Gwamna Francis Nwifuru wanda ya bayyana hakan a jiya yace an tabbatar da mutane 48 daga cikin 394 sun kamu da zazzabin Lassa tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2024.
washington dc —
Mutane 23 sun rasa rayukansu sakamakon cutar zazzabin lassa a jihar Ebonyi.
Gwamnatin jihar Ebonyi ce ta sanar da hakan yayin da take zayyano tsare-tsaren inganta walwalar al’ummarta da damarsu ta samun kiwon lafiya.
Gwamna Francis Nwifuru wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis yayin wani taro da ma’aikatar lafiyar jihar ta shirya a Abakaliki, fadar gwamnatin jihar, yace an tabbatar da mutane 48 daga cikin 394 sun kamu da zazzabin lassa tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2024.
Nwifuru ya bayyana cewa jihar na da shirin kafa asibitin kwararru a kowacce daga mazabun ‘yan Majalisar Dattawa 3 dake jihar domin bunkasa harkokin kiwon lafiya a yankunan karkara.