Cutar Ebola Ta Halaka Wani Karamin Yaro a Uganda

Wani yaro karami, dan shekaru biyar da haihuwa, ya rasu a Uganda sanadin kamuwa da cutar Ebola, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da aka samu mutuwar wani a sanadin yadda cutar take ratsa kan iyaka daga wata kasa ta shiga wata kasar.

Hakan na faruwa ne kamar shekara daya bayan bullar cutar ta Ebola a kasar Congo - Kinshasha wacce ke makwaftaka da kasar ta Uganda.

Ministar lafiya ta Uganda, Dr. Jane Ruth Aceng, ta ce daman an kai yaron assibiti ne jim kadan bayan da shi da mahaifansa suka tsallako cikin Uganda daga can Congo din.

Izuwa yanzu hukumomin kasar Uganda sun ce akalla mutane uku ne suka kamu da cutar ta Ebola a kasar.