Cutar Ebola na Bukatar Kula Cikin Gaggawa Domin Kaucewa Asarar Rai

Ma'aikata dake kula da masu cutar Ebola.

Sabanin maganganun da a keyi na cewa cutar ebola cuta ce da idan an kamu da ita ba makawa sai mutuwa amma batun ba haka yake ba domin mutane biyar cikin wadanda suka kamu da cutar sun mike kuma likitoci sun tabbatar basu dauke da kwayar cutar a jikinsu yanzu.

Rashin samun wadataccen maganin zima wanda ake cewa shi ne irinsa na farko mai maganin cutar ta ebola shi ma bai zame wani baban barazana ba.

Farfasa Abdulsalam Nasidi daya daga cikin shugabannin yaki da cutar ta ebola yayi bayani akan abun da suka yi wajen warkar da mutanen. Yace idan mutum ya kamu da cutar aka kuma kawoshi da gaggawa, idan an bashi maganin da ya kamata da yaddar Allah zai tsira da ransa. Idan an yi jinkiri ba'a kawo wanda ya kamu da cutar asibiti ba su ne suke tsira da kyar ko su mutu.

Dr Nasidi yace ba wai lallai duk wanda ya kamu da cutar zai mutu ba. Idan ba'a bada magani ba da sauri nan ne ake samun mace-mace da dama. Matakin farko shi ne a bada maganin zima domin ya hana kwayoyin yaduwa a jikin mutum.

Dangane da wadanda suke kwance yanzu yace babu wanda zai ce zasu rayu ko ba zasu rayu ba. Allah ne kadai ya san wannan.

Gwamnatin Amurka tace ta yaba da kokarin gwamnatin tarayya game da yakin da ta keyi da cutar ebola. Tace suna aiki kafada da kafada da hukumar kiwon lafiya ta duniya da kuma kasashen da cutar ta addaba. Haka kuma hukumar tantance ingancin magunguna ta kasa da kasa dake da ofis a Najeriya tace Najeriya ta taka rawar gani wajen yaki da cutar. Shugaban hukumar yace zasu cigaba da aiki da Najeriya wajen yaki da cututukan nan dake yaduwa cikin bani Adama.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Ebola na Bukatar Kula Cikin Gaggawa Domin Kaucewa Asarar Rai - 2' 58"