Cutar Dabbobi Ta Sake Lakume Rayukan Mutane Talatin A Nijar

Halaru Shaibu na ma'aikatar kiwon lafiya a Nijar

Rahotanni daga yankin Cintabaradun cikin jamhuriyar Nijar sun tabbatar cewa mutane dari da saba'in da ukku ne suka kamu da cutar dabbobi kuma tuni talatin daga cikinsu suka kwanta dama.

Sidi Muhammad Sidi wani dan jarida a Nijar ya shaidawa Muryar Amurka lamarin da ake ciki a yankin na Cintabaradun.

Ya bayyana cewa mutanen da suka kamu da cutar an kebe masu wuri domin dakile yaduwar cutar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar bada agaji ta Red Cross take cigaba da bada horo da fadakar da al'ummar yankin a kan illar cutar. Hakazalika horon ya shafi malaman makaranta talatin da matasa 'yan aikin sa kai na Red Cross a yankin.

Malam Alagoma Mamman Maiga mataimakin shugaban Red Cross na kasar Nijar gaba daya ya yiwa Muryar Amurka bayani. Ya ambaci wuraren da cutar ta riga ta shiga a yankin. Suna son mutane su gane cutar, illarta da abun da yakamata a yi cikin gaggawa.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Dabbobi Ta Sake Lakume Rayuka Talatin A Nijar - 2' 40"