Hukumomin kiwon lafiya a Maiduguri da ke jihar Borno a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 14 daga wata cuta da ake fargabar ta amai da gudawa ce.
Lamarin, a cewar hukumomin, ya faru ne a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri.
Tuni dai aka bude wasu asibitocin wucin gadi na gaggawa a sansanonin ‘yan gudun hijira na Dalori da Muna domin a dakile yaduwar cutar.
A karin bayanin da suka yi, jami’an kiwon lafiyar sun ce ba wai an samu bullar cutar a sansanonin na Dalori da Muna ba ne, sai dai an kai masu fama cutar can ne domin a dakile bazuwar cutar.
“Tun da wannan abu ya fara kusan sati hudu kenan mutane sun fi 200 wadanda suka kamu da cutar.” In ji kwamishinan kiwon lafiya a jihar ta Borno Dr. Haruna Misheliya.
Ya kara da cewa “wadanda muka sani sun rasu da amai da gudawa, mutane 14 ne.”
Misheliya ya kara da cewa daga mutum 14 da suka rasu, uku ne aka tabbatar cewa cutar amai da gudawa ce sanadinsu bayan wasu gwaje-gwaje da aka yi.
Saurari rahoton Haruna Dauda Biu domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5