Yayin da ake ta cece kuce game da sake fasalin tsarin Najeriya, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shaidawa Sahabo Imam Aliyu ra’ayinsa game da wannan batu, inda yake cewa ya aminta da cewa ba shakka akwai bukatar rage wa gwamnatin tarayya karfi ko kuma ayyuka, to sai dai kuma idan za’ayi sai anyi la’akari da wasu abubuwa.
Yace kowane bangare na da irin nauyin da ya kamata a barshi ya dauka domin kowannensu yana da hanyoyin warware kalubalan dake gabansa.
Gwamna Masari yace ba abinda ya hada gwamnatin tarayya da gina rijiyar burtsatse, ko kuma makarantar Firamare da dai ire-iren wadannan ayyukan.
Sai dai kuma ya nuna cewa amma fa ba kuma za’a rage wa gwamnatin ta tarayya karfi bane ta yadda bata da iko fiye da sauran rukunin gwamnatoci ba.
Ga Sahabo Imam Aliyu da Karin bayani: 2’26
Facebook Forum