Cristiano Ronaldo Yana Gaba Da Lionel Messi

Ronaldo da Messi

Shahararen dan wasan gaban nan na kasar Argentina, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, dake kasar Spain, Lionel Messi, mai shekaru 30 da haihuwa, ya jefa kwallonsa cikon na dari a raga a bangaren wasannin nahiyar Turai,

Messi ya samu wannan nasarar ne a jiya laraba a wasan da kungiyarsa ta Barcelona, tayi da Olympiacos, na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai 2017, a matakin rukuni, inda ta doke Olympiacos da kwallaye 3-1.

Messi, ne ya jefa kwallo ta biyu a raga a cikin mintuna na 61, da fara wasan.

Hakan ya bashi damar zamowa dan wasa na biyu a cikin jerin ‘yan wasan da suka fi zurara kwallaye a raga na yankin Turai a cikin wasanni 118, da ya buga ya jefa kwallaye 97, a (UCL) sauran 3 kuma a Super Cup.

Duk da wannan nasarar da ya samu yana bin bayan abokin hamayyansa Cristiano Ronaldo, na Real Madrid, wanda yake da kwallaye 113, a raga a wasannin 143, da ya buga na nahiyar Turai inda ya jefa 110, a (UCL).

Messi ya samu nasarar jefa kwallaye 82, a cikin 100 da yaci duk da kafar hagun, yayinda ya jefa kwallaye 14, da kafar dama sauran kwallaye 4, kuwa ya sakasu a raga ne da kai.

Your browser doesn’t support HTML5

Cristiano Ronaldo Yana Gaba Da Lionel Messi - 3'54"