Shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Portugal mai taka leda a kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo, mai shekaru 32, da haihuwa ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Ballon d' Or na shekarar 2017.
Cristiano Ronaldo, ya doke abokin hamayyarsa ne Lionel Messi na Barcelona wanda ya zo na biyu, shikuwa tsohon dan wasan Barcelona wanda ya kuma kungiyar Paris Saint-Germain na kasar Faransa Neymar, shi ya kasance a matsayi uku.
Cristiano Ronaldo, ya taimaka wa kungiyarsa ta Real Madrid wajen lashe kofin zakarun nahiyar Turai UCL da kuma lashe gasar La-Liga na kasar Spain, rabon kungiyar da wannan kofin tun 2012.
Haka kuma dan wasan ya kafa tarihi a bangaren gasar ta cin kofin zakarun nahiyar Turai UCL inda ya zamo dan wasan da yafi kowa zurara kwallaye a gasar
Kuma shine dan wasa na farko da ya jera wasannin shida a wasan rukuni na UCL yana saka kwallo a raga a kowace wasa da ya buga.
Wannan shine karo na biyar da Cristiano yake lashe wannan kyauta inda a shekara ta 2008, lokacin yana Manchester United ya fara lashe wa sai 2013, 2014, 2016 da 2017, duk a kungiyar Real Madrid.
Your browser doesn’t support HTML5