Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo, ya sake Kafa tarihi a bangaren gasar cin kofin zakarun nahiyar turai inda ya kasance dan wasa na farko da ya ci kwallaye 100 a gasar cin kofin zakarun turai duk kuma a kungiya daya.
Cristiano Ronaldo mai shekaru 33 da haihuwa ya samu cikon kwallon sa ta 100 ne a wasan da suka yi a ranar laraba tsakaninsu da Paris Saint-Germain, inda ya fara jefa kwallo a minti na 45 a bugun daga kai sai mai tsaron gida kafin tafiya hutun rabin lokaci 1-1 daga bisani ya jefa kwallon sa ta biyu a wasan a mintuna 83, andai tashi wasan 3-1 bayanda Marcelo ya sake jefa kwallo ta uku a minti na 86.
A cikin jerin ‘yan wasa 10 da suka zura kwallaye a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, Ronaldo yana kan gaba Kamar haka
Cristiano Ronaldo - Real Madrid 101
Lionel Messi - Barcelona 97
Raul - Real Madrid 66
Alessandro del Piero - Juventus 42
Thomas Muller - Bayern Munich 40
Didier Drogba - Chelsea 36
Ruud van Nistelrooy - Manchester United 35
Thierry Henry - Arsenal 35
Karim Benzema - Real Madrid 31
Wayne Rooney - Manchester United 30.
Shi ma Lionel Messi ya ceka wasannin sa na 300 a Barcelona a filin wasa na Camp Nou, dan wasan ya Kafa wannan tarihin ne a wasan da kungiyar ta yi da Getafe, ranar lahadi da ta gabata a wasan mako na 23 a Laliga, inda aka tashi canjaras 0-0.
A wasan da ya buga guda 300, ya samu kansa a wasanni 266 da aka fara dashi ya kuma taimaka wajan samun nasara a wasanni 246 ya kuma saka kwallaye 309.
A jimillar wasanni 300 da Messi ya buga a Camp Nou a Barcelona guda 201 a Laliga guda 56 Kofin zakarun turai ya kuma buga wasannin guda 34 a Copa del rey sai kuma guda 9 a Spanish Super Cup.
Your browser doesn’t support HTML5