COVID-19: Wasu Asibitocin Jirgin Ruwa Zasu Taimaka A Birnin New York

Adadin mutanen da suka mutu a jihar New York dake Amurka sanadiyyar annobar coronavirus a yanzu ya kai mutum 1,000. A yayin da gwamnatoci a fadin duniya suke kara daukar tsauraran matakai don dakile annobar.

Ana sa ran asibitoci a birnin New York zasu fara samun sauki, yayin da asibitin jirgin ruwan sojin ruwan Amurka, na tafi-da-gidanka ya isa birnin a yau Litinin, wanda zai samar da muhallin kula da masu cutar ta coronavirus, ta hanyar daukar masu bukatar kulawa ta musamman.

Makamancin wannan asibitin na jirgin ruwa da ake kira Mercy Ship shima daga rundunar sojin ruwan Amurka, ya soma kula da marasa lafiya a jiya Lahadi a bakin gabar tekun Long Beach dake birnin Los Angeles.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da tsawaita matakan kariya na nisanta jama’a da juna don kaucewa kara yaduwar annobar, matakan da ya kamata su kare aiki a yau Litinin, yanzu sai zuwa karshen watan Afrilu.

A yanzu Amurka ce ta fi yawan mutane masu dauke da wannan cuta ta coronavirus a fadin duniya.

Kasar Italiya dake da adaddin wadanda suka mutu mafi yawa, wadda kuma har yanzu take cikin tsauraran matakan hana zirga-zirga tsawon makonni, ta kara bada sanarwar mutuwar mutum 750 a jiya Lahadi, amma akwai alamun haske ta bangaren raguwar masu kamuwa da cutar.