COVID-19: Trump Ya Musanta Cewa Akwai Karancin Kayan Aikin Kariya

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya musanta rahoton binciken wani babban Sufeto-Janar da ya ce har yanzu ana ci gaba da samun karancin kayan aikin kariya ga ma’aikatan asibiti da kuma kayan gwajin cutar COVID-19.

"Ba daidai ba ne." Amsar da Shugaban ya bada kenan a jiya Litinin 6 ga watan Afrilu a lokacin da aka yi masa tambaya game da rahoton mukaddashin babban Sufeto-Janar din hukumar kula da lafiya da lamurran jama’a. Trump ya kuma ce, "mun yi karin gwaje-gwaje kuma mun sami sakamako fiye da ko'ina a duniya."

Trump ya nuna wa manema labarai wata kididdiga dake nuna gwaje-gwaje miliyan 1.79 na cutar COVID-19 da aka gudanar a Amurka. Ya kara da cewa adadin yana karuwa da mutane dubu 125 a kowacce rana.