A yayin da kasashen duniya suka yi shagulgulan ranar ruwa ta duniiya a jiya Lahdi 22 ga watan Maris masu fauitikar samar da wadatar ruwan sha ga jama’a a jamhuriyar Nijer sun gargadi mahukunta da su maida hankali akan maganar tsaftar ruwa don murkushe cututtukan dake yaduwa sanadiyar kazanta.
Ranar ruwa ta duniya a bana ta zagayo ne a wani lokaci da kasashen duniya ke fama da annobar cutar coronavirus, abinda ya sa kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin ruwan sha irinsu REJEA ke amfani da wannan lokaci don kara ankarar da mahukuntan kasar muhimmancin ruwa a rayuwar bil adama, musamman idan aka yi la’akari da cewa tsafta na daga cikin manyan matakan riga kafin wannan sabuwar cuta.
Tsaftar muhalli da tsaftar abubuwan bukatun jama’a na daga batutuwan da mahukunta ke zuba ido a kai don tabbatar da tsaftar ruwan sha a Nijer, inji babban daraktan ma’aikatar tsafta a ofishin Ministan albarkatun ruwa da tsafta, Dan Dobi Moussa Mahaman.
Samar da wadatar ruwan sha mai tsafta na daga cikin kudurorin da majalisar dinkin duniya ke fatan cimmawa kafin nan da shekarar 2030, abinda ya sa kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatocin kasashe masu tasowa musaman a nahiyar Afrika suka dage haikan don ganin sun fita kunyar alkawalin da suka dauka a karkashin yarjejeniyar ODD.
A saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5