COVID-19: Kocin Super Eagles Ya Makale A Kasar Faransa

A halin da ake ciki, kocin kungiyar kwallon kafa na Super Eagles, kuma dan kasar Jamus Gernot Rohr ya makale a kasar Faransa, abinda ya sa ba zai samu damar dawowa Najeriya ba, saboda dokar hana shiga kasar da aka sanya a matsayin matakin dakile yaduwar cutar coronavirus. Sai dai koch din yana tuntubar ‘yan wasan Super Eagles ta hanyar yanar gizo.

A daya gefen kuma, Rohr yana jira ya ga ko mahukuntan Najeriya zasu sabunta kwantaraginsa, saboda zai kare a watan Yulin wannan shekarar ta 2020.

Rohr, wanda dan asalin kasar Jamus ne, ya jagoranci kungiyar kwallon Super Eagles a gasar kwallon kafa ta duniya da aka gudanar a Rasha a shekarar 2018, tare da gasar kasashen Afrika da aka gudanar a kasar Masar a bara, inda Najeriya tazo na uku.

Amaju Pinnick

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ita ma ta bi sahun kasashen duniya wajen yaki da yaduwar cutar COVID-19. A wani sakon bidiyo, shugaban kwallon kafar Najeriya Mr. Amaju Melvin Pinnick, ya ja kunne ‘yan Najeriya da kuma masoya wasan kwallon kafa akan su bi dokokin da hukumar lafiya ta bayar don yakar yaduwar annobar cutar coronavirus.

Mr. Pinnick ya bukaci masoya wasan kwallon kafa da su bi umurnin hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma umurnin gwamnatin kasa na tabbatar da bin kai’dojin tsafta.

A wata sabuwar sanarwa da hukumar kwallon kafar Najeriya ta fitar ranar Litinin 30 ga watan Maris, ta bukaci a dage da addu’oi sabili da halin da masu sana’ar buga tamola suka shiga ciki, inda ake sace su domin neman kudin fansa da kuma yadda suke mutuwa sanadiyar hadurran mota.

Shugaban hukumar Mr. Amaju Melvin Pinnick ya ce ‘yan wasan kwallon kafa guda uku sun rasa rayukansu a wani hadarin mota da ya afku a kan hanyar Benin, ciki har da Ifeanyi George dake buga kwallo a kulob din Enugu Rangers.

‘Yan wasan da aka sacen sune Dayo Ojo na kungiyar Eyimba, da kuma Benjamin Iliyomadae na kungiyar Abia Comets.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Abdulwahab Mohammed.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Kocin Super Eagles Ya Makale A Kasar Faransa