A yau Juma’a rahotanni sun ce kamfanin Dow Jones dake auna hada-hadar kasuwar hannayen jari ya bayyana samun karamar riba jim kadan bayan kada kararrawa. Kamfanin S&P shima ya samu riba ta kimanin rabin kaso cikin dari, kana NASDAQ ya samu riba ta kasa da kashi biyu cikin dari.
Kasuwannin kasashen Turai da Asiya suma sun cira bayan jawabin shugaban Amurka Donald Trump da yammacin jiya Alhamis na shirye-shirye farfado da tattalin arzikin kasar.
Haka kuma rahoton Gilead, wani kamfanin hada magunguna dake kokarin samar da maganin annobar COVID-19 a Amurka ya kara taimakawa wajen farfado da kasuwanin hannayen jari.
Ko a yammacin jiya Alhamis cibiyar bincike ta asibitin koyarwar jami’ar Chicago, ta ce mutum 125 da aka gwada ba maganin annobar COVID-19 sun warke cikin kankanin lokaci, sakamakon shan maganin da kamfanin na Gilead ya sarrafa. Wannan maganin da aka sarrafa mai suna “Remdisivir” an yi shine don gwaji.
Ga dukkan alamu kasuwannin Asiya basu motsa ba duk kuwa da labaran da ke nuna cewa tattalin arzikin China ya fadi warwas a farkon wannan shekarar ta 2020, karon farko cikin shekaru 100.