COVID-19: Jihar Sokoto Ta Rufe Iyakokinta Sakamakon Kwararowar 'Yan Nijer

Matakan da hukumomin Najeriya ke dauka don hana yaduwar cutar coronavirus sun hada da hana zirga-zirga a wasu sassan kasar.

Jihar Sokoto dake yankin arewa maso yammacin Najeriya, kuma mai makwaftaka da Jamhuriyar Nijer na daga cikin jihohin da suka rufe kan iyakokinsu har tsawon makonni biyu.

Wannan kuma na faruwa ne a daidai lokacin da jihar ke fuskantar kwararowar ‘yan Nijer, bayan da rahotanni suka tabbatar da cewa mutane da dama sun kamu da cutar coronavirus (COVID-19) a Nijer, wasu kuma sun mutu. Wasu daga cikin ‘yan Nijer da suka shiga jihar Sokoto sun ce suna daukar matakan kariya ne kamar yadda hukumomin lafiya suka umarci jama'a su yi.

Alhaji Abubakar, wani mazunin jihar Sokoto, ya yi kira ga hukumomin jihar da su dauki matakan dakile yaduwar cutar, ta hanyar tabbatar da cewa an duba duk wanda zai shigo kasar sosai.

Da yake maida martani, ASP Muhammad Abubakar Sadik, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ya ce suna bin dukkan iyakokin jihar domin tabbatar da kariya.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Lamido Abubakar Sokoto.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Jihar Sokoto Ta Rufe Iyakokinta Sakamakon Kwararowar 'Yan Nijer