Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Yi Hakuri Ku Ci Gaba Da Zama a Gida – Buhari 


Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

A yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ya kai 323, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ci gaba da zama a gidajensu domin kare lafiyarsu daga kamuwa da cutar Coronavirus.

A wannan makon ne wa’adin mako biyu da gwamnati ta umarci da a zauna gida yake karewa.

Bisa wannan sakon dai, alamu sun nuna cewa gwamnati bata da niyyar dage wannan dokar nan kusa.

Gwamnatin jihar Niger ta kafa wata doka da zata fara aiki a yau wadda za ta tilasta wa 'yan Jihar zama a gida na makkoni biyu.

Hakan na faruwa ne bayan da aka samu rahoton mutum na farko wanda ya kamu da cutar a jihar.

Wannan dokar dai na ta janyo ce-ce ku-ce, inda mutane da dama ke kukan yunwa da kuma talauci.

Mallam Rabilu Mani wani mazaunin legas ne kuma ya shaida wa Muryar Amurka cewa talauci da yunwa na daga cikin abubuwan da ke sanya mutane kin bin wannan dokar.

Ya ce “idan ace babu yunwa da talauci a Najeriya, idan gwamnati ta ce a zauna gida na watanni biyu ma, duk zamu zauna.”

Rahoto na baya-bayan nan da cibiyar dakile cututtuka a Najeriya, NCDC ta fitar ya nuna cewa an samu Karin mutum 5 da ke dauke da wannan cutar.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba da yawan masu cutar da mutum 176.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG