A wani kwarya-kwarayan biki da aka yi a shelkwatar hukumar gidajen yarin birnin tarayya Abuja, Ministan harkokon cikin gidan Najeriya, Ogbeni Rauf Aregbesola ya ce fursunoni saba’in daga cikin 2,670 da za a sallama yau Talata 9 ga watan Afirilu, daga gidan yarin Kuje dake babban birnin kasar suke.
Da yake wa Muryar Amurka karin bayani, Ministan Shari'ar Najeriya Abubakar Malami ya ce kamar kowanne dan Najeriya, suma fursunoni suna da hakkin gwamnati ta karesu a irin yanayin da ake ciki, shi ya sa gwamnati ta dauki wannan matakin da nufin rage cunkoso a gidajen yarin kasar don guje wa yaduwar cutar coronavirus da kuma rage hasarar rayuka.
Ministan ya kuma ce gwamnatin Najeriya ce ta biya wa fursunonin kudin tarar da aka yi masu. Sannan ya yi kira ga wadanda ke da hali da su rungumi al'adar taimaka wa marasa galihu da tsautsayi ya sa aka kai su gidan kaso.
Shugaban hukumar gidajen yarin Najeriya Jafaru Ahmed ya ce fursunonin da da za a sallama masu kananan laifuka ne, wadanda kuma suke gab da kammala wa'adin hukuncisu.
Wasu daga cikin wadanda aka sallama sun nuna farin cikinsu tare da shan alwashin zama ‘yan kasa na gari.
Saurari Karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5