COVID-19: Adadin Mace-Mace a Amurka Zai Iya Ninka Na Yanzu Sau 50

Daraktan Cibiyar Nazarin Cututtuka Masu Yaduwa Dr Anthony Fauci

A Amurka, babban masani kan cututtuka masu yaduwa, Dr. Anthony Fauci, ya yi hasashe cewa Amurkawa dubu 100,000 ne ko fiye da haka zasu iya mutuwa a sanadiyyar annobar Coronavirus.

Hakan na nufin wato zai ninka adadin mace-mace na yanzu sau 50.

Fauci ya fada wa kafar yada labarai ta CNN cewa a yanzu mai yiwuwa Amurka na da miliyoyin masu dauke da COVID-19, hakan na nuna cewa annobar ta yadu sosai a kasar.

A yanzu a hukumance an bayyana adadin 135,000 na wadanda aka tabbatar na dauke da cutar da kuma 2,370 na wadanda suka mutu, duk da cewa adadin na saurin karuwa a kullun a kasar.

Fauci, wanda shi ne darektan Cibiyar Nazarin Cututtuka Masu Yaduwa ya yi watsi da bayyanan Shugaba Donald Trump masu cewa ana iya sassauta umurnin zama a gida da kuma bayar da tazara.