Wani sabon rahoto daga cibiyar kula da hana yaduwar cuttuttuka ta Amurka ya ce adadin wadanda ke mutuwa da cutar covid-19 ya ninka har sau goma sha biyu, ga wadanda suke fama da wadansu cututuka kafin kamuwa da cutar fiye da sauran mutane da ke dauke da cutar kawai.
Manya daga cututtuka da ke haddasa mutuwa sosai sun hada da ciwon zuciya da ciwon suga da na huhu.
Wani bincike da jami’ar Chicago ta gudanar na nuni da cewa, kashi 11 cikin 100 na Amurkawa bakar fata na da aboki ko dangi daya da ya mutu daga coronavirus idan aka kwatanta da kaso 4 cikin 100 na fararen fata.
Masana a harkar lafiya sun bayana rashin samun kyakyawar kulawa na daga cikin dalilan, duk da cewa akwai wadansu dalilan da suka haddasa hakan.
A wani hasashe daga wani gwaji da Tsangayar Lafiya ta Jami’ar Washington ta gudanar na cewa mace-mace a Amurka sanadiyar coronavirus ka iya kai dubu 200,000 nan da zuwa watan Octobar bana.