COVID -19: Mutum Na 19 Ya Mutu a Amurka

Wasu jami'an kiwon lafiya a Amurka

Hukumomi a Amurka sun tabbatar da mutuwar mutum na 19 yayin da jami’an gwamnatin Shugaba Trump suka ce suna fadi-tashin ganin an hanzarta samar da kayayyakin gwaje-gwajen cutar coronavirus.

A jiya Asabar adadin wadanda cutar ta harba a sassan rabin adadin jihohin Amurka ya haura zuwa 400.

A baya-bayan nan jihohin Pennsylvania, Indiana, Minnesota da Nebraska suka bayyana mutane na farko da suka kamu da cutar, yayin da Florida ta samu mutum biyu da suka mutu.

Jami'an gwamnatin Amurka sun yi watsi da sukar da kwararru a fannin kiwon lafiya ke yi cewa, an bata lokaci wajen samar da kayayyakin gwaje-gwajen cutar, idan aka kwatanta da matakan da kasashe irinsu Korea ta Kudu da Jamus suka dauka.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO dai ta ci gaba da yin kira ga kasashe da su tashi tsaye.

“Muna kira ga kasashe da su nemo, su yi gwaji, su kuma kebe wadanda suka kamu da cutar tare da ba su kulawa, a kuma bi diddigin wadanda suka yi cudanya da su,” inji Shugaban hukumar ta WHO kenan, Tedros Adhanom Gebereyesus.

Ya zuwa jiya Asabar dai, adadin mutanen da suka kamu da cutar a duk fadin duniya ya haura 100,000, yayin da mutum kusan 3,500 suka mutu.