Coronavirus: Babban Bankin Najeriya Ya Gabatar Da Kudirin Rage Haraji

Babban bankin Najeriya na CBN ya fito da wasu tsare-tsare don magance mummunan tasirin da cutar coronavirus ke yi akan kasuwanci da tattalin arzikin kasar.

Tsare-tsaren dai sun hada da rage kudin haraji kan wasu kayayyaki guda 9, daga kashi 9 zuwa 5 cikin 100 a ko wacce shekara. Haka kuma babban bankin zai ware wasu kudade don tallafa wa matsakaitan 'yan kasuwa da wadanda cutar ta shafa.

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa wannan mataki ne mai kyau idan har aka aiwatar da shi yadda ya dace.

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta tabbatar da karin mutum 5 dake da cutar a jiya Laraba 18 ga watan Maris, jami'an lafiya kuma na ci gaba da karfafa tsabtar kai da kuma guje wa shiga cunkoson jama'a.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Coronavirus: Babban Bankin Najeriya Ya Gabatar Da Kudirin Rage Haraji