Gwamnatin jihar Legas ta bada umarnin hana tarukan ibadah da suka haura mutane 50 a masallatai da majami’u. Haka kuma gwamnatin ta ce daga ranar litinin mai zuwa zata rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu domin rigakafin cutar coronavirus da ta kama mutane 8 a jihar.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce tuni ta gudanar da taruka tare da shugabannin manyan addinan kasar biyu domin daukar wannan mataki na riga kafi. Kwamishinan yada labarai na jihar Legas Gbenga Omotoso, ya ce gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne domin hana yaduwar cutar coronavirus kuma su na fatan samun nasara a yaki da cutar.
Wasu daga cikin ‘yan Najeriya sun yaba da wannan mataki da gwamnatin jihar Legas ta dauka yayin da wasu ke ganin ya yi tsauri.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Neja ta musanta rahotannin dake cewa, wasu mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, a ta bakin Kwamishinan lafiyar jihar Dr. Makun Sidi Makun. Kwamishinan ya bayyana cewa tabbas mutane biyu sun rasu amma daya sakmakon cutar hawan jini, dayan kuma sakamakon cutar tarin fuka wato TB.
Ya zuwa yanzu dai hukumomi da dama na ci gaba da daukar matakan da suka dace na magance yaduwar cutar coronavirus da ta kama mutane 8 a Najeriya yanzu.
saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum