Coronavirus: An Ba Amurkawa Shawara Su Fara Rufe Fuskokinsu

Wani ma'aikacin Lafita rufe da fuskarsa domin kare yaduwar gutar coronavirus a Yemen 17, Maris 2020. REUTERS/Khaled Abdullah

Gwamnatin Amurka ta bai wa al’umar kasar shawara da su fara saka kyallen kare fuskokinsu domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Hukumar kare yaduwar cututtuka ta CDC ce ta fitar da sabbin ka’aidojin kare yaduwar cutar wacce Shugaba Donald Trump ya sanar a ranar Juma’a.

Sai dai Trump ya jaddada cewa, matakin ba dole ba ne domin shi kansa ba zai bi ba.

“Za ku iya yi, in kun ga dama kuma ba sai kun yi ba. Amma ni dai ba zan yi ba.” Trump ya fadawa mandma labarai.

Sai dai Dr. Jerome Adams, Shugaban Likitocin fida a Amurka ya ce, saka kyallen kare hanci da baki, ba gurguwar shawara ba ce a kokarin da ake yi na kare yaduwar cutar, saboda da yawa daga cikin masu dauke da ita ba sa nuna wata alama.

Ya zuwa ranar Juma’a, sama da mutum 275,000 ne ke dauke da cutar ta COVID-19 a Amurka, yayin da mutum 7,000 suka mutu a cewar Jami’ar Johns Hopkins.