Bullar annobar cutar coronavirus na daga cikin matsalolin da suka maida hannun agogo baya ga batun samar da magunguna da kuma jinyar masu HIV AIDS a wurare da dama a fadin duniya, ciki har da jihohin Adamawa da Taraba a kasar Najeriya. Kamar dai a ce ne: ana ta corona wa ke ta HIV AIDS.
Wannan na zuwa ne yayin da aka yi bikin Ranar Tunawa da masu dauke da kwayar cutar ta HIV AIDS a fadin duniya. Hasalima, hakan na daga cikin abubuwan da aka lura da su gabanin jiya da ta ke ranar tunawa da masu dauke da mugunyar cutar da ma bayan nan.
Yayin da a fadin duniya ake cigaba nemo bakin zaren magance matsalar annobar cutar coronavirus ko COVID 19, wasu da wannan annoba ta fi shafa sune wadanda ke dauke da kwayar cutar HIV AIDs. Al’amarin na shafarsu ta fuskoki biyu: Na farko, saboda rashin karfin garkuwar jiki, coronar na iya saurin kama su; sannan kuma saboda maida hankali da aka yi kan batun coronar, an daina kula da masu fama da HIV AIDS don haka cutar na masu illar gaske.
Hasali ma, sakamakon annobar ta COVID -19 da kuma raja’ar da aka yi kanta, masu dauke da kwayar cutar HIV AIDS da dama ne suka rasa rayukansu walau sabili matsala ta kai tsaye kamar rashin samun magani ko kuma matsalolin da ba na kai tsaye ba, irin dokokin da aka kafa na hana zirga zirga, wanda hakan ya yi ta haifar da wasu matsalolin da su ka shafe masu fama da HIV AIDS din ta bangarori daban daban.
Malama Farah James dake zama jami'ar tuntuba wato kodinata ta masu dauke da kwayar cutar ta HIV AIDS a jihar Adamawa, wadda har ila yau ita ce hadimar gwamnan jihar ban batun masu dauke da wannan cutar, ta bayyana halin da suka shiga sakamakon annobar coronavirus. Ga dukkan alamu akwai bukatar a gaggauta waiwayarsu musamman wajen sukunin zuwa karbar maganin ko kuma a rib araba masu gida gida.
Ya yin da wasu ke boye cutar, ita kuwa Magret Daniel da ta kamu da cutar shekaru fiye da goma da su ka gabata, ta ce lamarin ba na boyewa ba ne saboda babu wanda ya so kamuwa da cutar kuma babu wanda ya san gobe banda Allah, wanda kuma shi ya kamata a bar masa komai.
Dr Chubado Abubakar, Babban Sakataren Hukumar Yaki da Yaduwar Kwayar cutar ta HIV AIDS a jihar Adamawa, ya bayyana irin matakan da suke daukawa. Haka ma Dr Garba Danjuma shugaban hukumar kula da masu dauke da cutar ta HIV AIDS a jahar Taraba.
Ga Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton ta sauti:
Your browser doesn’t support HTML5