Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Yi Kira Kan Kula Da Lafiyar Kwakwalwa


Antonio Guterres
Antonio Guterres

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatoci da su maida hankali a kan ayukan kula da lafiyar kwakwalwa yayin da jama’a a duniya suke fama da annobar coronavirus.

“Bayan shafe gwamman shekaru da yin watsi da kuma rashin ingantattun ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa, annobar COVID-19 yanzu haka ta afkawa iyalai da al’ummomi da karin matsalar kwakwalwa,” in ji Babban Sakataran Majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres a yau Alhamis.

Ya kara da cewa, ma’aikatan lafiya, tsoffi da matasa da kuma wadanda suke fama da rashin lafiyar kwakwalwa ko wadanda suke fama da yaki ne ke cikin hadari sosai.

Guterres ya fada cewa Majalisar Dinkin Duniya ta sha alwashin samar da yanayi da kowa zai iya samun tallafi akan bukatun kwakwalwa a duk inda yake, ya kuma bukaci gwamnatoci da kungiyoyin sa kai da ma’aikatan lafiya da kuma sauran mutane da su hada kai cikin gaggawa don magance matsalar rashin lafiyar kwakwalwa a lokacin wannan annoba.

Sakon na Babban Sakataran Majalisar Dinkin Duniya ya biyo ne bayan da Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, kwayar cutar ya zuwa yanzu ta kama sama da mutum miliyan 4 da dubu dari 3, kuma ta kashe kusan dubu dari uku, da za ta iya zama kamar kwayar cutar HIV da ke haddasa cutar Sida ko Kanjamau wato AIDS.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG