Coman Ya Kifar Da Mafarinsa

  • Murtala Sanyinna

Kingsley Coman

Ya zura kwallo da ta kifar da kungiyar da raine shi, ta kuma baiwa kungiyarsa ta yanzu nasara.

Manazarta lamurran wasanni na ci gaba da jinjina ga matashin dan wasan Bayern Munich Kingsley Coman, wanda ya zura kwallon da ta kifar da tsohuwar kungiyarsa ta PSG, ta kuma baiwa kungiyarsa ta yanzu damar lashe gasar zakarun Turai ta bana.

Coman ya kwashe tsawon shekaru kusan 10 a PSG, inda ya fara tun daga kwalejin kungiyar ta horar da kananan ‘yan wasa har ya buga mata wasanni 4 a matakin babbar kungiyar.

Coman dan kasar Faransa mai shekaru 24, ya janyo hankalin manazarta kwallon kafa, akan yadda kungiyoyi ke sakin matasan ‘yan wasan da suka horar, kana daga bisani su kasance wani abu har su zame musu ala-kaki wata rana.

Kingsley Coman

Coman ya bar PSG a shekarar 2014, ya koma Juventus inda ya lashe gasar Serie A sau 2, kafin komawarsa kasar Jamus, inda tauraruwarsa ta kara haskakawa musamman a karshen wannan kakar wasannin.

Ga baki daya dan wasan ya sami lashe kofunan gasannin lig 9, 2 a PSG, 2 a Juventus da kuma 5 a kungiyarsa ta yanzu wato Bayern Munich.