COVID-19: Najeriya Za Ta Kashe N400B Kan Rigakafi

Ana yi wa wata ma'aikaciyar jinya rigakafi a New York

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya tace gwamnatin kasar na bukatar kudi kimanin nera biliyan 400 don kaddamar da allurar rigakafin cutar korona.

Kudaden dai za ayi amfani da su ne domin yiwa kashi 70 cikin 100 na al'ummar Najeriya rigakafin da yawansu ya kai kimanin miliyan 211.

Da yake yiwa shugaban majalisar dattawa bayani game da shirin, ministan lafiya Osagie Ehanire yace a shirye gwamnatin tarayya take domin ceto 'yan Najeriya, duba da cewa an shiga zagaye na biyu na annobar korona.

shugaban-faransa-emmanuel-macron-ya-kamu-da-annobar-covid

birtaniya-ba-za-ta-ci-gaba-da-zama-fursunan-covid-19-ba---johnson

najeriya-an-sami-mutum-na-farko-da-ya-rasu-sakamakon-coronavirus

Mai sharhi kan lamuran yau da kullum Bashir Baba yace wannan wani salo ne na kamfatar dukiyar talaka a yayin da matsalar tsaro ke addabar kasar.

Da yake tsokaci kan lamarin Aliyu Shamaki yace tunda annobar cutar korona ta shiga ake fitar da makudan kudaden don yaki da cutar amma har yanzu 'yan Najeriya basu gani a kasa ba.

Hoton tallafin maganin da madagascar ta baiwa Nijar domin yakar coronavirus

A nasa bangaren masanin kimiyar siyasar tattalin arziki a jami'ar Abuja Dr. Farouq Bibim Farouq yace duk da lamarin yana da kyau amma kudin yayiwa irin kasashe masu tasowa kamar Najeriya nauyi.

Yanzu dai za'a jira aga yadda lamarin zai kasance lokacin da mutane suka fara sabawa da barazanar annobar.

Saurari cikakken rahoton Hawa Umar cikin sauti

Your browser doesn’t support HTML5

CODVID19: Najeriya Za Ta Kashe N400B Kan Rigakafi:3:00"