Shugaban jam'iyyar ta CNDD-FDD mai mulkin kasar Pascal Nyabenda yace duk da kiran da jamiyun adawa suka yi jama'a sun nuna cewa sun gummace mulkin dimukuradiyya fiye da juyin mulki.
Sai dai a waje daya rahotanni sun bayyana cewa jama'a da dama ba su fito zaben na ranar Litinin wanda ya kai har yammacin ranar. Haka kuma Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya bayyana damuwarsa game da wannan zaben.
Suko jami'an zabe sun ce har zuwa lokacin da aka rufe runfunar zabe ba a sami wata tangarda ba duk kuwa da yake anji karar harbin bindiga da tashin gurneti a babban birnin kasar wato Bujumbura.
Nyebenda ya karyata cewa jama'a basu fito ba, yace 'yan kasar Burundi sun fito gwargwadon hali domin jefa kuria, sannan masu zabe na cewa zaben na cewa an gudanar da shi cikin adalci da walwala ba tare da sa ido ba.