Amma kama daga shugaban PDP Alhaji Adamu Muazu har zuwa wadanda suka samu tikitin tsayawa takara a inuwar jam'iyyar sun sauya salon kemfen suna cewa Allah ne ya san gaibu maimakon da can da suke nunawa babu wanda ya isa ya kayar dasu zabe ko kuma akidar nan ta a mutu ko a yi rai.
Dan takarar neman shiga majalisar wakilai daga PDP din Ismaila Muazu Hassan yace siyasar da zasu yi, siyasar kishi ce ba siyasar kwadayi ba. Akan ko watakila wannan karon PDP zata zama marasa rinjaye a duk majalisun kasar domin adawa tayi karfi sai yace ai zabe na Allah ne. Wancan karon ma an yi adawa idan kuma an yi adawa a wannan karon sai kuma me. Yace sai an yi an gwada sai kuma abun da Allah ya nuna. Yanzu zata yi wuya a ce domin kaifin adawa 'yan adawan zasu ci zabe, idan an yi zaton haka kuskure ne.
PDP ce ke jan ragamar mulkin kasar da kuma shugabancin majalisun tarayyan guda biyu kodayake kwana kwanan nan kakakin majalisar wakilai Aminu Waziri Tambuwal ya canza sheka zuwa jam'iyyar adawa.
Ibrahim Bello Rigachukun yace abun mamaki shi ne tunda ake majalisa ba'a taba samun kakakin da 'yan majalisar daga duk jam'iyyun suna kauna ba kamar Aminu Tambuwal.
A nashi bangaren madugun tafiya Janaral Buhari ya sauya salon muamala da jama'a inda yanzu ya kan kaiwa sauran abokan tafiyarsa ziyara da yiwa sauran jama'a murmushi a wajajen taro. Ya ma nuna kwarin gwuiwa cewa samun canjin gwamnati a wannan karon mai yiwuwa ne.
Dangane da cewa Janaral Buhari soja ne kuma bai dace da dimokradiya ba sabili da tsatstsauran ra'ayi sai yace halin soja iri-iri ne domin su ma mutane ne.
Amma shi ma shugaba Jonathan yana kokarin kare kambun jam'iyyarsa na mulki inda Janaral Buhari a takara karo na hudu ke ganin alamun nasara.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5