Cin Kudin Makaman Yakar Boko Haram Na Cikin Laifuffukan Yaki, Inji Lauya Falana

Wasu Dakarun Najeriya Bayan Darkake 'Yan Boko Haram a Bama

Tuntuni dai ake ta allan baku da maganar badakalar sayen makaman yaki da ‘yan ta’addar Boko Haram da ake zargin manyan jami’an gwamnatin Najeriya da wawure kudaden a karkashin jagorancin Sambo Dasuki, babban mai bawa tsohon shugaba Goodluck Jonathan shawara ta fannin tsaro a lokacin mulkiinsu.

To wannan badakala dai ta ja an caccafke jama’a da dama ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa da ake zargin suna da hannu wajen wannan aika-aikar ta turmushe kudaden da aka ware don sayen makaman da sojojin kasar zasu yi amfani da su don yakar ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram, wadanda ke hallakawa da jikkata dubban ‘yan Najeriya da makwabtanta a kullum.

Kotun hukunta laifuffukan yaki da ci zarafin bil’adama da take birnin Hague ta shahara wajen hukunta shugabannin duniya da suka yi makamantan laifuffukan da suka ci zarafi ko gallazawa al’umma. Wanda ta hukunta shugabanni da dama daga kasashen duniya musamman daga kasashen Afirka da Gabas ta tsakiya.

Babban lauyan nann na Najeriya mai rajin kare ‘yancin bil’adama wato Cif Femi Falana, ya gabatar da wata wasika ga mai gabatar da kara Fatu Bensuda, ya bukaci Kotun duniya da ta yi bincike tare da hukunta duk wanda ke da hannu a karkatar da kudaden Najeriya da aka ware don tsare kasar daga ta’addanci.

Ya bayyana cewa, kudaden da aka ware don yaki da kungiyar ta’addar Boko Haram, amma wasu tsirarin jami’an gwamnati suka karkatar da su don muradan kawunansu. Wanda Lauyan yake kallon abin daidai da aikata laifukan yaki kasancewar dubban jama’ar da ya kamata su sami tsaro daga ‘yan ta’addar sun mutu saboda rashin iya karesu da aka yi sakamakon sace kudaden.

Femi Falana ma ya kara da cewa, ya kamata ita ma tsohuwar Ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta fuskanci tuhumar wannan badakala bisa gazawarta na kare sibare wadannan kudade sama da biliyan biyu ta dalar Amurka, wadanda aka ce an samo sune daga asusun ajiyar marigayin Shugaban kasar Janar Sani Abacha.

Wani Lauya Aliyu Umar ya bayyanawa wakilinmu Babangida Jibrin yadda yake kallon lamarin a shari’ance.

Your browser doesn’t support HTML5

Cin Kudin Makaman Yakar Boko Haram Na Cikin Laifuffukan Yaki, Inji Lauya Falana - 2'26"