Awal Musa Rafsanjani mai fafutikar ganin an yi mulki mai adalci da kiyaye dukiyar jama'a yace Najeriya tana da dokoki da ka'idodi koda shugaban kasa baya nan dole ne a bi dokokin.
Idan akwai wasu shugabannin gwamnati da ba zasu bi dokokin gwamnati ba ke nan gyaran da ake son a yi ya zama banza, inji Rafsanjani. Yana harsashen idan Shugaba Buhari ya gama mulkinsa ya tafi kasar na iya komawa cikin cin hanci tsamo tsamo.
A cewar Mukhtari Adamu Yarima Sarkin Babarawa batun cin hanci da rashawa a Najeriya tun dama can babu abun da ya canza. Ya ta'alanka gwamnatin Buhari da tsohuwar jiya cikin sabuwar kwalba. Yace yawancin wadanda suka zabi shugaba Muhammad Buhari mutane ne da suka saba da almundahana. Sun yi zarmiya can baya. Sun yi watanda da dukiyar jama'a. Su ne kuma suka hau jirgin Buhari suka daure masa gindi ya hau gwamnati.
Mukhtari yace cin hanci a karkashin gwamnatin Buhari ba wai sai ya fita ba. Yana cikin gida ma ana yi. Injishi an zargi wasu shugabannin dake tare dashi kamar Kyari da babban sakataren fadarsa da kuma batun Babachir wanda aka zarga da yin almundahana.
Yace akwai abubuwa da yawa da suke da nasaba da cin hanci da rashawa ana yi kuma ana kallo. Sai dai 'yan Najeriya su cigaba da addu'a Allah ya kawo shugabannin nagari amma Muhammad Buhari sun gama dashi, acewar Mukhtari.
To sai dai gwamnatin Najeriya tayi watsi da zarge zargen. Shaban Ibrahim Sharada hadimin shugaban kasa na musamman kan harkokin watsa labarai yace babu wani ministan da zai kashe kudi ba tare da amincewar majalisar zartaswa ba saboda haka zargin cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari bashi da tushe.
Ga cikakken bayani daga rahoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5