A satin da ya gabata ne rundunar jami'an 'yan sandan Najeriya ta sallami wasu jami'an ta masu aikin bada hannu a kan hanya su biyu a birnin tarayya Abuja daga aiki sakamakon kama su da laifin amsar cin hanci da rashawa na kudi Naira dubu goma sha biyar da suka amsa a hannun wani mai abin hawa.
Da yake jawabi, kwamishinan 'yan sanda mai kula da ofishin undunar jami'an dake yankin ya bayyana sunayen 'yan sandan su biyu da suka kama wani direba a kusa da kasuwar Wuse, wanda suka zarga da kin tsayawa yayin da wutar hanya ta tsayar da shi.
Rahotanni sun bayyaa cewa ma'aikatan sun tsare mutumin na lokaci mai tsawo inda suka bukaci ya biya kudi, duk da cewa ya fada masu bashi da kudi a lokacin. Jami'an sun takurawa direban inda suka bi shi har ATM, inda ya ciro masu kudin daga ajiyar sa ta banki.
Mujallar Daily post, ta wallafa cewa yayin da suka koma bakin aiki, daya daga cikinsu ya manta wayarsa ta hannu, wadda direban yayi amfani da ita wajan kai karar jami'an biyu a ofishin kai korafi na jami'an 'yan sandankuma aka umurce su da su kasance a ofishin ba tare da bata lokaci ba.
Daga karshe rahotanni sun bayyana cewa jami'an su karyarta afkuwar lamarin amma aka nuna masu shaida, wato wannan waya da dayansu ya manta a cikin motar direban, inda daga nan ne aka tasa keyarsu zuwa dakin da ake tuhumar ma'aikatan da suka aikata laifuka.